Qamshi Complete Hausa Novel

Qamshi 11-15

Sponsored Links

 

 

 

*✨QAMSHI  11-15 ✨*

 

 

*✍️RASHOW*

 

 

tun k’arfe uku na dare na farka nayi istihara kamar yanda na sama raina Zanyi najima Ina sallah har asuba tayi, tashi nayi na gabatar da nafula wato salatul Fajr sannan na zauna a gurin nayi lazumi har aka kira assalatu mikewa nayi na gabatar da sallah asuba.

 

na jima Ina kai kuka na ma Allah buyi gagara misali bayan na idar nayi azkar din safiya don bani wasa da azkar domin shine takobin mumini Seda na shafa addu’ar sannan na mike na ninke abun sallan na miyar dashi yanda nake adanawa sannan na durkusa a agaban gado na nadaga bakin katifar da take kan gado,hannu nasa a karkashin katifar na dauko wannan bakin laida da Hajiya Diddy ta karbomin agun alhajin mu.

mayar da katifar nayi kamar yanda yake sena zauna a bakin gadon na kunce daurin da nayi ma bakin laidar sekuwa ga tulin kudi sun bayyana.

 

idona na zaro waje don kuwa tunda nazo duniya bantab’a ganin kud’i masu yawa tsiraran su hakaba,wani irin yawu na hadiye baki bude.

gyara zama na nayi da kyau sannan na mik’e da sauri naje na kulle kofar d’akina sannan na dawo na zauna na zazzage kud’in akan gado wani irin Kallo na kebin kudin.

Seda na gama bin kud’in da Kallo sannan na fara rabasu Kashi Kashi,na cire yan dubu dubu da ban, se yan d’ari biyar biyar ma daban,sannan na fara aikin k’irgasu dalla dalla don banison asamu matsala.

bani nagama kirga kud’in nan ba har saida naga rana ta b’ullo ta jikin labulen window na sannan na sarara musu, a hakan ma da naso nasake tisa k’irgawa kar wani ya mak’ale ajikin d’an uwansa .

 

cikin hanzari na futo na nufi cikin kitchen dake cikin falon mu,na kunna gas wanda na dan tara riban da nake samu nasiyo mana don amfanin mu duk da d’an karami ne, daura ruwan bak’in tea nayi na mishi hadin komai sanna na futa daga kitchen din na nufi d’akin da kaji na suke don na kwashe Kwan da sukayi karsu fasa su shanye,Se da na basu abinci da ruwa sannan na futo daga d’akin kajin.

 

bayan na gama bama kaji ruwa da abinci na dibo kwai din da sukayi naje na a dana shi acikin gurin da na warewa domin adana d’anyar kwai, gurin na mayar dashi kamar store don Yana da kofa harda makulli da nasa akayi min shi.

 

kwai (egg) na kulla a cikin laida baka,na nufi cikin gidan mu wato sashin da matan alhaji mu suke.

 

Sashin Mami Zulay amaryan alhaji mu na fara shiga, a haraban sashin nata na hango ta a duke da amalar wani abun takeyi a tsakar gidan na duk’a na gaishe ta da girmamawa don muna shiri sosai da ita, don ita tafi sauran matan baba na kirki ga hakuri, tana da Yar ta guda daya ta mace.

 

“Mami na ashe kin   tashi “?

 

Murmushi Maam Zulai tayi tace.

 

“na tashi khubra, yau dai ban bari maganin nan ya rinjaye niba.

 

murmushin nima na mayar mata tare da sake gaishe ta.

 

“Antashi lafiya Mamin mu yaya karfin jikin?”

 

“lapiya law khubra jiki yayi sauki sosai ,yaya hajiya ta tashi dafatan komai lpia.

 

nayi murmushi nace komai lafiya Mami,amma Mami ina Zahra take ta barki kike tsaye anan ke kadai?

 

Nayi tambayar Ina Kallon aikin da Mami takeyi na Shirya musu abun karyawa da takeyi.

 

Dafa kaina tayi tace.

 

“karki damu diyar arzik’i zahra suna ciki nima abu nafuto zan dauka kika ganni anan.

 

Kaina na daga mata sannan na mike nace.

 

“Mami na allah yakara miki lpia.

 

” amiin Khubra nagode da gaisuwa.

 

Ajiye mata laidar dake hannu na nayi a kasa kusa da ita nace.

 

” Mami na ga kwai ba yawa a soyama Zahra, Mami na acigaba da mana addu’a ma wannan sana’ar nawa.

 

murmushi Mami Zulai tayi tana me cewa.

 

“in banda abunki khubra yaya za’ayi ki debo kayan jauran ki haka,ai semu karya jarin,dakin bari har sekin dad’a bunqasa tukunna seki bamu alakoron.

 

tayi maganar da sigar zolaya tana dariya.

 

dariyan nima nayi nace.

 

kai Mami na yanzu kwai guda goma ne dayawa ?

 

ai addu’ar ku na cigaba da kuke mana akoda yaushe bazai taba bari kasuwar mu tayi qasa ba, don haka Mami na Kimin addu’a da bakin ki me albarka.

 

Murmushi Mami ta sake yi tace.

 

“to shikenan khubra mun gode Allah yasa nan gaba abud’e mana k’aton gidan gona Allah kuma ya kauda idon makiya arzik’i yata bunkasa.

 

” amiin Mami na, maybe hajjin bad’in bad’ad’a dake za’aje irin wannan addu’a haka.

 

nafada Ina dariya.

 

“kajimin yarinya.

 

wato bama na bad’in nan ba har sekin karamin da bad’ad’a ko.?

 

Dariya nayi Ina tafiya nace.

 

” to mami banda abunki har yau she na bunkasar da zan miki alkawarin zan biya Miki kujeran makka shekara me zuwa? kinsan ni bani karya don asoni.

 

kai Mami ta daga tace.

 

” hakane kuma.

 

“to muna matukar godiya da wannan kyautar .

 

Futa nayi a sashin Maam Zulay na nufi sashin Maam Saratu, daga bakin komar falon ta na tsaya nayi sallama yaran ta ne suka amsa min,shiga cikin falon nayi na samu guri daga kan kujerun da suke falon na zauna kamar yanda naga yaran ta guda biyu sunyi,yaa Kamal dana gani a falon na fara gayarwa Rabe kuma ya gaisheni tunda shidin na girme shi duk da ba wani girma na can bane.

duk rashin jituwar da mukeyi da matan Alhajin mu bashi ya hana mu yaran gidan girmama junan mu ba.

 

Maam Saratu tafito daga cikin dakin ta tana cewa.

 

” a’a Yaya nakejin kamar muryan yar gadaran gidan nan a dakin nan?

tana me k’arasa futowa cikin falon.

 

basarwa nayi kamar banji taba,zama tayi a daya daga rub’abb’un kujerun ta da suke falon, duk da bawani Yara ne da Maam Saratu ba amma kayan dakin ta yafi na kowa lalace wa agidan.

sanda ta yi kusan minti uku da zama sannan na dubeta nace.

 

“Maam barka da safi da fatan antashi lafiya.

 

” lafiya law alhamdulillah na tashi.

 

” ai na d’auka maganar ma bazaki iya bane kin wani hakimce akujera sekace fulanin gidan sarki.

 

murmushi nayi wanda ya zamemin jiki in bason magana shi nakeyi ma mutum don hakan ma ya wadatar basai nace komai ba,hakan kuma yakan qular da wanda nayi domin shi, don sukance raini ne hakan.

 

ba tare dana ce mata komai ba na mike na isa  kusa da kafarta na ajiye baqar laidar dake hannu na nace.

 

“Maam ga kwai a soya masu rabe amma sadaka ne.

 

mikewa nayi na nufi kofa domin futa a sashin……

 

” keee dawo ki d’auki Kwan ki, kamar ke har nice zaki kalla don bakida kunya kicemin sadaka kika bamu kwai, da yake ance miki mu mabara tane ko.?

 

bance mata komai ba na juyo da nufin na d’auki laidar kwai din  caraff Rabe ya d’auke laidar Kwan kamar walqiya yana cewa.

 

“dan Allah Adda khubra kiyi hakuri ki barmana wallahi mu muna son kwai din zamu soya mun gode Allah ya qara budi tunda mama tace bata so kinga shikenan semu had’a da nata mu soya sema yafi auki, mun gode my Adda.

 

Dafa kafadar shi nayi Ina sake murmushin da Maam ta tsana nace.

 

“cewa zakayi allah shikarb’a don sadaka na bayar d’an kanina.

 

murmushin na kuma yi na juya nace.

 

Byee yaa Kamal.

 

Nayi tafiya ta cikin isa da izza kamar yanda suke cewa shiyasa suke kirana da qamshin gadara.

 

Ina jiyo muryan Rabe yana murna suna tafawa da Yaa Kamal.

 

b’angaren Maam Tabawa na shiga da sallama na iske surayya abakin murhu tana wura wuta.

 

“Adda khubra Ina kwana?

harara na galla mata.

 

bakinta tayi sauri rikewa tace.

 

” au sorry Adda khubra antashi lpia.

 

murmushi me dauke da harara nayi mata nace.

 

“lafiya law,yarin ya duk ranar da kika sake cemin ina kwana Sena zubar miki da rub’abb’un hakoranki kaf a qasa.

 

Ina me wucewa na nufi cikin falon Maam Tabawa, Seda nayi sallama tareda d’aga labulen falon na shiga ciki.

k’afata na sanya acikin falon amma Jina nayi kamar wacce na sanya kafar a cikin yashi.

haka na daure na shiga na sameta a baje itada sauran yaranta guda biyu, guri na samu a Saman kujeran falon na zauna,duk yaran suka hada bakin su gurin cewa.

 

“Adda khubra antashi lafiya .

 

murmushi nayi musu nace.

 

” lafiya law Alhamdulillah,dafatan kuntashi lafiya kuma?

 

na amsa musu tare da kallon fuskar Maam Tabawa wacce ta mele baki tareda kauda kanta gefe don tafi sauran matan baba na din rashin wayewa.

 

” Maam Tabawa barka da safiya antashi lafiya .

 

“law.

 

tace min atakaice don duk cikin matan alhajimu tafi nuna min rashin kauna don dai kawai Diddy tafi nuna soyayyar ta a kaina.

 

hakan dana gani ne nima yasani na mike na ajiye mata qullin laidar dake hannu na a gaban ta nace.

 

” Maam ga kwai asoya ma kanne na sadaka.

 

naki guda biyune aciki sauran duk nasu ne.

 

banjira cewar taba nayi fucewata yaran ne ma naji suna cewa.

 

” Adda allah ya amfana .

 

komawa sashin mu nayi na sauke ruwan black tea din dana daura akan gass,juye wa nayi a tea flas guda biyu,sannan na fasa kwai da dan yawa na yanka albasa, na Sa danyar tumatur nad’an bubbuga tafarnuwa kad’an bame yawaba na sanya maggi Sena dauko dafaffen zogalen dana tsinka a tsakar gidan mu na wanke na dafa na ajiye agefe shine yanzu na dauko na zuba ahadin kwan na barbad’a Curry kad’an sannan na daura pan din akan gass na kunna na soya mana na jera namu akan tebur din dayake falon, sena sauran ragowar flas din akan tire na nufi sashin Alhajin mu.

 

A bakin kofar falon na tsaya nayi sallama.

 

daga ciki naji ya amsa min tare da bani izinin shiga.

Seda na ajiye turen hannuna akan tebur sannan na durkusa nace.

 

“Baba Alhaji Barka da safiya da fatan ka tashi lpia.

 

Kallo na baba me zuma yi tare da ajiye jaridan hannun shi yace.

 

” lafiya law na tashi khubra Yaya kika tashi keda hajiyar taki?

 

murmushi nayi Ina tsiya ya mishi black tea a cup nace.

 

“duk lafiya law muka tashi Baba.

 

Na bashi amsa Ina mika mishi cup din tea.

 

Karban cup din yayi yana cewa.

 

” mashà Allah yau kuma  wani abun dad’in nasamu haka ne Yar  hajiya?

 

Karamar dariya nayi nace.

 

“kai alhaji kwai nefa da ruwan shayi ba wani abu ba.

 

na bashi amsa Ina me dad’a gyara zama na a qasa kusa dashi.

 

” Kai amma nagode sosai qamshin Hajiyar ta kamar kinsan Ina neman black tea dinan don inason na futa yanzu sabida muna da wani taron gaggawa daya taso min,Allah yayi miki albarka Allah ya baki masu miki kema,Allah ya jikan mahaifiyar ki.

 

” Amin nace idona yana me dan tara qwalla na tunawa da mahaifiya ta da nayi.

 

shiru falon yayi ganin hakan da Alhajin mu yayi ne yayi gyaran murya don kauda shiru ya dubeni yace.

 

akwai abun da kike sone Khubra ?

Naga yanayin ki kamar da akwai abunda kike so ki gaya min.

 

girgiza kaina nayi Ina wasa da yatsun hannu na nace.

 

“a’a Baba, daman godiya nazo zanyi na aikan da Hajiya Diddy tabani jiya,daka bata ta bani shine nazo godiya.

 

 

Bude baki Baba me zuma yayi yace.

 

” oho! kice dai toshiyar baki kika kawomin da kwai.

 

yayi maganar da raha don ya mantar dani damuwar dana shiga na tunawa da mahaifiya ta danayi.

 

yana maganar yana dariya, nima dariyan nayi nace.

 

” a’a Baba Alhaji nidai godiya nazoyi zalla.

 

Ina me dariyan nima.” Baba Alhaji nagode sosai allah yakara rufa asiri yasa kafi haka Allah kuma yajikan mahaifa yabamu ikon jin qanku.

 

“amiin khubra shiyasa nake me alfahari dake a Koda yaushe saboda kwazonki dakuma sanin ya kamatan ki da hangen nesa,duk da kasan cewar ki mace nasan halinki na kuma San zaki iya, amma zan dan dada rokonki daki nutsu ki bada himma ga kasuwancin ki tunda angama karatun sakandiren sekuma muta addu’a har Allah yafuto da mijin aure kafun nan zanso ki cigaba har lokacin da zaki samu mijin.

 

Kaina na duqar a qasa nace.

 

“nagode sosai Baba alhaji.

 

amma baba alhaji ashe daman kana da kudi dayawa dayawa haka ?

 

Kama baki Baba me zuma yayi yace.

 

” oh khubra kincika bin kwaf,inada kudi daidai gwargwado,nuna wane bansonyi don nasan halin matana, kema don na auna hankalinki ne, naga a kaji guda a shirin har kinsan ki gyarama hajiya Diddy sashinta kin sanya mata tayals a dakin ta,kin saya muku gass na girki kin gyara daki daya daga cikin d’akunan dayake cikin falon kin mayar dashi kitchen, ga abun tafasa ruwan zafi kin sanya mata a bayin ta don Kar tayi alwala da ruwan sanyi a lokacin sanyin na, duk kin dauke nauyin da ya dace ace nine yakamata nayi mata don neman albarka, amma se gazawa ta fado kaina ke kuma da kike diyata kika dauki wannan babban aikin ladar,Sam baki barinta da yunwa kafin matana su tashi su girka su Kai mata ke harkin gama kin bata taci ta koshi,ga kuma kulawa da ita da kikeyi wanda ko ita ta haifeki iyakan biyayyar da zaki mata kenan,kinga kuwa kin cancanci na baki sama da miliyan dubu ma idan Ina dashi,ba Wai kuma don nafi sonki bane a cikin yara na bane, sedai kinsan ance rai yana son mai kyautata mata, kuma nima a shirye nake na bada gudun mawana ga duk wanda ya maida hankalin shi ga neman na kanshi don banison mutuwar zuciyar da yaran nan sukeyi,duk wanda ya maida hankali ya nemi abun yi to yazo nikuma nayi alqawari zan bashi Jari,amma bazan taba bada kwandala na don a salwantar da ita ta hanyar da bai kamata ba,ki duba kiga yayun ki babu abunda sukasa a gaban su sedai su shiga su fita se gantalin bin abokai da suka sanya agaba, yanzu har kananun ma sun dauki halin manyan.

 

Yayi maganar muryan shi tana rawa, alamun abun ya dade yana damun shi acikin ranshi.

 

Seda ya dauki tsawan mintuna Sannan yace.

 

” wannan kud’in da kika ga na bayar a baki, kud’in filina ne dayake garin dungal shine na sayar wancan satin akan zan dad’a a kasuwancin kiwon shanun da nakeyi,se kuma ganin da nayi kin mai da hankali ga kiwon kajin da kikeyi ne kuma Allah yasa ma abun albarka shine nace barin baki mugani ko za’a dace,don naga nauyin da kika daura a kanki yayi miki yawa gashi har naji Hajiya Diddy tace ta saukemin abincin gidana Wai naki ma ya wadatar, naga kajin naki kuma  sun kasa ma wannan d’awainiyar.

 

Dakatawa yayi da maganar shi kamar me nazari sannan yace.

 

“da fatan bazaki bani kunyaba Khubra,zakiyi abunda ya dace dama wanda nake hasasowa anan gaba.

 

Kaina na daga idona yana me cikowa da kwalla muryata a sanyaye nace.

 

“in sha Allah Baba zan maida hankali naga nayi abunda kud’in bazai lalace ba,sedai Baba Alhaji Ina neman Karin addu’ar ka domin ganin haske ma lamari.

 

Murmushi Baba Alhaji yayi sannan yace.

 

” addu’a kullum acikin yimuku mukeyi Khubra, sedai zamu dad’a akan Wanda mukeyi in sha Allah, allah yamuku albarka gaba d’ayanku.

 

“Amin nace nayi masa sallama nadawo sashin Hajiya Diddy.

 

 

 

 

https://chat.whatsapp.com/GvGr3Qu8WXnC0f7ORdteIW

 

 

*Rashow*

07052100719  only chat.

Leave a Reply

Back to top button